Home Labaru Kiwon Lafiya Korona Ta Kama Karin Mutum 21 A Najeriya Ranar Litinin

Korona Ta Kama Karin Mutum 21 A Najeriya Ranar Litinin

102
0

Hukumar ɗakile yaɗuwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 21 da suka kamu da cutar korona a Najeriya lanar Litinin.

NCDC ta ce alƙalumman sun nuna mutum shida ne suka kamu da cutar a Legas, jihar da cutar ta fi bazuwa, sai jihar Cross Rivers da aka samu mutum biyar, sai jihar Ondo mai mutum uku, a jihar Kaduna ma an samu  ƙarin mutum ɗaya haka ma a jihar Bauchi.

A halin yanzun dai jimillar mutum dubu 214 da 113 cutar ta shafa a Najeriya amma dubu 207 da 297 sun warke yayin da cutar ta kashe mutum dubu 2 da 976 a Najeriya.