Home Labaru fursuna 262 sun tsere a jos

fursuna 262 sun tsere a jos

144
0

Mahukunta a Najeriya sun ce fursunoni 262 ne suka tsere daga gidan yarin Jos, babban birnin jihar Filato bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai gidan yarin.

Wata sanarwa da hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya ta fitar ranar Litinin ta ce fursunoni tara sun mutu yayin da aka rasa ma’aikacin gidan yarin daya, kana aka kashe dan bindiga guda yayin harin da ‘yan bindiga suka kai a kurkukun ranar Lahadi da almuru.

Sanarwar ta kara da cewa an kama fursunoni goma da suka tsere, yayin da har yanzu ake neman 252, sai dai babu wani labara game da ainihin ‘yan bindigar da suka kai harin da kuma dalilin su na yin hakan.

Tun da farko, hukumomin sun ce an ritsa da maharan a cikin gidan yarin, amma daga bisani sun ce sun tsere bayan kubutar da wasu fursunoni a harin.

Leave a Reply