Home Labaru Korona: An Aikata Fyaɗe Samada 100 A Kowace Jiha Yayin Dokar Kulle

Korona: An Aikata Fyaɗe Samada 100 A Kowace Jiha Yayin Dokar Kulle

460
0

Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce an samu rahotannin fyaɗe sama da dubu 3 da 600 a Nijeriya yayin da ake cikin dokar kullen anobbar korona

Mataimakiyar Sakataren majalisar Amina Mohammed ta bayyana haka, ta na mai nuna damuwar ta game da yawaitar cin zarafi mai alaƙa da jinsi a Nijeriya.

Amina Mohammed ta bayyana haka ne, yayin ƙaddamar da wani taron ƙara wa juna sani a kan cin zararfin mata da ƙananan yara, inda ta ce za ta cigaba da aiki da Ma’aikatar Harkokin Mata ta Nijeriya domin ƙara tattara bayanai game da cin zarafin mata.

An dai gudanar da taron ne a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai da Ma’aikatar Harkokin Mata ta Nijeriya.

Leave a Reply