Home Labaru Korafi: ‘`Yan Sanda Na Shan Wuya A Ƙarƙashin Tsarin Fansho Na Bai-Daya

Korafi: ‘`Yan Sanda Na Shan Wuya A Ƙarƙashin Tsarin Fansho Na Bai-Daya

8
0
Majalisar wakilan ƙasa ta kammala karatu na biyu kan wani ƙudurin doka da ke neman a cire `yan sanda daga tsarin fansho na bai-ɗaya da aka sanya mafi yawan ma`aikatan ƙasar a ciki.

Majalisar wakilan ƙasa ta kammala karatu na biyu kan wani ƙudurin doka da ke neman a cire `yan sanda daga tsarin fansho na bai-ɗaya da aka sanya mafi yawan ma`aikatan ƙasar a ciki.

Masu goyon bayan ƙudurin dokar sun bayyana cewa `yan sanda na shan wahala a ƙarƙashin tsarin, saɓanin sojoji da ma’aikatan waɗansu manyan hukumomin gwamnati.

Wasu ‘yan sanda da suka yi ritaya na ta zanga-zanga a baya-bayan nan don nuna rashin amincewa kan tsarin fenshon da suka ce na yi musu kisan mummuƙe.

Hon Shehu Mohammed Koko, ɗan majalisar wakilai ne, ya bayyanawa maneama labarai cewa bai san dalilin da yasa aka bar ‘yan sanda a cikin tsarin fensho na bai daya ba, bayan tun a lokacin da aka yi wannan doka a lokacin mulkin shugaba Obasanjo, an cire sojoji da jami’an hukumar leken asiri ta SS daga ciki.

Hon Shehu Mohammed Koko, ya ce a yanzu za a yi kokari a cire ‘yan sandan daga cikin tsarin fensho na bai daya wanda su kansu ‘yan sandan ke kuka da shi.

Tuni wasu daga cikin tsoffin ‘yan sandan da ke kan tsarin fensho na bai daya a Najeriyar, suka yi kira ga mahukunta da su cire su daga tsarin da suka ce yana cutar da su.