Home Labaru Labarun Ketare Kisan Nijar: ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 37

Kisan Nijar: ‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 37

56
0
Niger Killings3

Rahotanni sun ce fararen hula 37 ne aka kashe a yankin yammacin Nijar a hare-haren da ƴan bindiga masu da’awar jihadi da ake tunanin daga Mali suka tsallako suka kai.

Kamfanin dillacin labaru na AFP ya ce majiyoyi daga yankin da suka tabbatar da harin a yau Talata, sun ce ƴan bindigar sun abka ƙauyen Darey-Daye da ke cikin yankin Tillaberi saman babura a yammacin Litinin suka buɗe wa mutane da ke aiki a gona wuta.

Kuma cikin waɗanda aka kashe sun ƙunshi mata da ƙananan yara 13, kamar yadda wani jami’i a yankin ta tabbatarwa AFP.