Home Labaru Daukar Mataki: Buhari Zai Gana Da Shugabannin Tsaro Na Najeriya

Daukar Mataki: Buhari Zai Gana Da Shugabannin Tsaro Na Najeriya

58
0
Service-Chiefs

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro a fadar sa a ranar Alhamis.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce shugaba Buhari wanda ya dawo daga London a ranar Juma’a zai gana da shugabannin tsaron ne domin tsara tsare-tsaren kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro da ke gaban su.

Ganawar ta ranar Alhamis a cewar sanarwar, ta shafi sanar da shugaban ƙasa kan ci gaban da aka samu.

Sanarwar ta ce jami’an tsaron Najeriya sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da ƴan fashin daji da sauran masu aikata laifuka da suka addabi ƙasar waɗanda hakan ke sa suke miƙa wuya.