Home Labaru Kisan Filato: Shugaba Buhari Ya Gana Da Sheikh Dahiru Bauchi A Abuja

Kisan Filato: Shugaba Buhari Ya Gana Da Sheikh Dahiru Bauchi A Abuja

234
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin Sheik
Dahiru Usman Bauchi a fadar sa da ke Abuja.

Duk da cewa babu wani tartibin abin da su ka tattauna, amma
rahotanni sun ce hakan ba ya rasa nasaba da kisan da aka yi wa
matafiya a jihar Filato.

Kimanin mutane talatin ne su ka mutu sakamakon harin da ake
zargin ‘yan kabilar Irigwe sun kai a kan motar matafiyan a
birnin Jos, amma sun musanta wannan zargi.

Kungiyoyin farar-hula sun nuna takaici da alhini game da
mummunan kisan-gillar, wanda hatta mahukunta sun zargin ‘yan
kabilar Irigwe da aikatawa.

Shugaban kungiyar amintattu na gamayyar kungiyoyin Arewa
Nastura Ashiru Sharif, ya ce sun yanke kauna game da ikirarin
da mahukunta ke yi cewa za a hukunta mutanen da ake zargi da
kashe matafiyan.

Leave a Reply