Jam’iyyar APC ta dakatar da shugaban ta na rikon kwarya na karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa Sulaiman Adamu sakamakon zargin shi da aikata laifi.
Ana dai tuhumar Sulaiman ne da laifin zagin shugaba Muhammadu Buhari, don haka majalisar gudanarwa ta jihar ta kafa kwamitin ladabtarwa na mutane bakwai a karkashin jagorancin Sa’idu Naira domin binciken zargin da ke yi wa Sulaiman Adamu da sauran abokan tafiyar sa.
Jam’iyyar APC ta kafa kwamitin ne bayan wani faifai da aka samu, wanda aka ji wani ya na cewa ‘Ina ma a ce shugaba Muhammadu Buhari ya mutu.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar APC ta fitar ta hannun sakataren yada labaran ta Mohammed Abdullahi, ta ce a matsayin su na jam’iyya, sun samu wani faifai da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda aka ce ya fito ne daga wajen taron wasu ‘yan jam’iyyar a Yola.
A cikin faifan dai an ji Adamu na cewa, in da so samu ne cutar Coronavirus ta kashe shugaba Muhammadu Buhari mataimakin sa Yemi Osinbajo ya hau kujerar mulkin.
You must log in to post a comment.