Home Labaru Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ware Wa ‘Yan Sanda Kudin Sayen Man Fetur

Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ware Wa ‘Yan Sanda Kudin Sayen Man Fetur

36
0

Gwamnatin tarayya ta amince da ware naira biliyan hudu, domin sayen Man da motocin ‘yan sanda za su yi aiki da shi a jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.

Ministan ma’aikatar harkokin ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ya tabbatar da haka a Abuja, inda ya ce kudin da aka ware a kasafin shekara 2021, su ne karon farko da aka ware wa ‘yan sanda kudin man fetur a Nijeriya.

Ya ce Majalisar zartarwa ta tarayya, kwanakin baya ta amince da Ayyukan Musamman na ‘yan sanda, don inganta gaskiya da rikon amana, tare da zama wata hanyar samar da kudaden inganta ayyukan ‘yan sanda.

Dangane da sabon tsarin albashin jami’an ‘yan sanda da Shugaba Buhari ya yi alkawari, Dingyadi ya ce umurnin Shugaban kasa na samar da sabon tsarin albashi mai inganci zai fito nan ba da jimawa ba.