Home Labaru Kididdiga: Sama Da Mutane Miliyan 100 Ne Ba Su Da Katin Shaidar...

Kididdiga: Sama Da Mutane Miliyan 100 Ne Ba Su Da Katin Shaidar Dan Kasa

267
0
Aliyu Abubakar, Shugaban Hukumar Katin Shaidar Dan Kasa
Aliyu Abubakar, Shugaban Hukumar Katin Shaidar Dan Kasa

Shugaban hukumar katin katin shaidar dan kasa Aliyu Abubakar, ya ce kimanin mutane milyan 100 ne ba su da katin dan kasa a Nijeriya.

Abubakar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi a wajen taron Majalisar Sarakunan arewacin Nijeriya karo na 6 da ya gudana a kaduna.

Taron dai, an shirya shine domin wayar da kan al’umma a kan mahimmancin mallakar katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce mafi yawan wadanda ba su mallaki katin ba matalauta ne da marasa galihu.

Abubakara ya kara da cewa, tattara bayanan shaidar ‘yan kasa zai taimaka wajen inganta hakkokin al’umma, tare da habbaka tattalin arzikin Nijeriya, sannan zai bada dama wajen samun kididdigar ‘yan kasa da kuma tallafawa tsare-tsaren gwamnati.

A na shi jawabin shugaban hukumar hana fasa kwabri ta kasa Hameed Ali, ya ce matakin da gwamnati ta dauka na kulle iyakokin Nijeriya ya taimaka wajen magance ayyukan ta’addanci da shigo da kaya ta barauniyar hanya.

A karshe Hameed Ali ya ce gwamnatin tarayya ta tilasta wa jami’an Kwastam bin dokokin kungiyar ECOWAS, domin kare tattalin arzikin Nijeriya daga ayyukan ‘yan fasa kwauri.