Home Labaru Majalisar Sarakuna: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani Game Da Hukucin Kotu

Majalisar Sarakuna: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani Game Da Hukucin Kotu

358
0

Gwamnatin jihar Kano ta mai da martani a kan hukuncin da babbar kotun jihar ta yanke a kan dokar kafa majalisar sarakuna a jihar.

A cikin wata sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya fitar, ya ce hukuncin kotun bai shafi sabbin masarautun jihar da aka kirkira ba.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Talatar da ta gabata ne wata babbar kotun jihar a karkashin mai shari’a Tijjani Badamasi ta yanke hukuncin dakatar da gwamna Ganduje daga kafa majalisar sarakunan jihar, tare da  tsida a ranar 17 ga watan Disamba domin cigaba da sauraron karar.

Kwamishinan ya kuma zargi makiya sabbin masarautun da sauya ma’anar hukuncin, tare da cewa za su sha kunya idan kotu ta yanke hukuncin karshe a kan lamarin.

Garba ya kara da cewa, ba tantama bangaren gwamnati ne zai yi nasara, saboda an bi doka wajen kirkirar sabbin dokokin masarautun.

A karshe ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su zauna lafiya tare da cigaba da biyayya ga doka da oda musamman a lokacin  da kotu ta zartar da hukuncin.