Home Labaru Ketare: Hukumar Leken Asiri Ta Kame ‘Yan Jarida 4 A Afghanistan

Ketare: Hukumar Leken Asiri Ta Kame ‘Yan Jarida 4 A Afghanistan

155
0

Hukumar leken asiri ta Kasar Afghanistan, ta kame wasu ‘yan jaridu guda hudu bisa kai ziyara wani gari da ‘yan kungiyar Taliban ke zaune.

An zargi ‘yan jaridun da yada jita-jitar makiya a cewar masu ruwa da tsaki na Hukumar.

‘Yan jaridun wanda ‘yan asalin kasar Afghanistan ne suna tsare a garin Kandahar da ke Afghanistan, bayan dawowar su daga wani gari mai suna Spin Boldak a ranar litinin.

Garin Spin Boldak na iyaka da kasar Pakistan wanda kungiyar Taliban ta kwace tun farkon wata Yulin da muke ciki.

Kafafen yada labarai na kasar sun yada cewa ‘yan jaridun sun je binciken wasu rahotanni da gwamnati ta yada na cewa ‘yan kungiyar Taliban sun hallaka mutane da dama a garin, zargin da ita kungiyar mai tayar da kayar baya ta musanta.

Duk wata yada jita-jita da ke nuna goyon baya ga ‘yan ta’adda wanda kuma ya sabawa bukatun kasar Afganistan laifi ne”, a cewar mai magana da yawun Ministan Cikin Gida na kasar, Mirwais Stanikzai.

Kungiyar yan jaridu ta Afghanistan ta yi kira ga Gwamnatin kasar da ta saki wadanda aka kama da gaggawa.

Mai magana da yawun Kungiyar Taliban, Muhammad Naeem, ya ce ‘yan jaridun guda hudu sun kai ziyara garin Spin Boldak domin su binciki rade-radin cewa a kashe mutane a garin.

Leave a Reply