Home Labaru Kasar Saudiyya Ta Daƙile Harin Da Houthi Ta Kai Filin Jirgin Abha

Kasar Saudiyya Ta Daƙile Harin Da Houthi Ta Kai Filin Jirgin Abha

22
0
Houthi Attack Saudi

Rundunar sojin Saudiyya ta ce ta daƙile wani harin jirgi marar matuƙi da ƴan tawayen Houthi suka ƙaddamar a Yemen.

Saudiyya tayi zargin cewa an kai harin ne da nufin lalata filin jirgin sama na Abha.

A yayin harin Mutum huɗu sun ji rauni sakamakon tarkacen jirgin da ya fado daga sama.

Tuni dai ‘Ƴan tawayen suka ci gaba da kai hare-hare kan iyakokin ƙasashen biyu.

Inda Suka ce suna mayar da martani ne kan hare-haren saman da rundunar sojin haɗakan da Saudiyya ke jagoranta ke kai wa a yankunan da mayaƙan Houthin ke iko da su.