Home Labarai Kasafin Naira Biliyan 7.2 Na Gyare-Gyaren Fadar Shugaban Ƙasa Sun Yi Kaɗan...

Kasafin Naira Biliyan 7.2 Na Gyare-Gyaren Fadar Shugaban Ƙasa Sun Yi Kaɗan – Umar

323
0

Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa ya ce, kasafin Naira biliyan 21 da Miliyan 100 da aka ware wa fadar sun yi matukar kaɗan.

Tijjani Umar, ya na magana ne dangane da Naira biliyan 7 da miliyan 200 daga cikin kuɗaɗen da za a kashe a ɓangaren gyare-gyare da kula da fadar shugaban kasa.

Kasafin shekara ta 2023 dai, ya ware naira biliyan 21 da miliyan 100 domin kashewa a Fadar Shugaban Ƙasa, inda daga cikin kuɗaɗen za a kamfaci Naira biliyan biyu a sayo sabbin motoci, sannan a kashe naira miliyan 644 wajen gyaran Karamin Ofishin Shugaban Ƙasa da ke Legas.

Nijeriya za ta ciwo bashi na sama da naira tiriliyan 8, kuma za ta biya bashin sama da naira tiriliyan 6 duk a cikin shekara ta 2023.

Masana da daman a ganin cewa, Nijeriya ta ƙara shiga mawuyacin halin da ake canja Dalar Amurka 1 a kan Naira 900, alhali lokacin da shugaba Buhari ya hau mulki ba ta wuce Naira 200 ba.

Leave a Reply