Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen gyara jam’iyyar PDP, domin ita ce za ta gyara Najeriya.
Makinde ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a nan Abuja a lokacin ƙaddamar da kwamitin gwamnoni na jam’iyyar, da kuma fitar da tsare-tsaren cibiyar (PDI).
wadda cibiya ce ta bincike da aka assasa tun a shekarar 2000 domin bincike da tattara bayanai da horarwa da sauran su.
Makinde ya ce jam’iyyar ce za ta iya gyara Najeriya, inda ya ƙara da cewa, za su gyara PDP, ita kuma sai ta gyara Najeriya.
Ya ce a yanzu da suka fara fuskantar 2027, akwai buƙatar PDP ta samar wa ƴan Najeriya wata damar daban, kuma Najeriya na buƙatar gyara da tsari mai kyau ta hanyar jiran PDP ta kawo musu wani zaɓin.
ya ce tun a 1999 yake cin moriyar PDP, sannan ya ce ba zai so ya gurɓata rijiyar da ya sha ruwa a cikin ta ba.
A nasa jawabin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya nanata buƙatar da ke akwai na haɗin kai a PDP.














































