Shugaban kasa Bola Tinubu, ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar murnar cika shekara 78 a duniya.
Atiku Abubakar, wanda ya kasance abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023, ya cika shekara 78 a jiya Talata 26 ga watan Nuwamban 2024.
Shugaba Tinubu ya tura wa Atiku sakon taya murnar ne ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da Sadarwa, Sunday Dare.
A cikin sakon, Bola Tinubu ya yaba wa Atiku Abubakar kan rawar da ya taka a tsarin dimokuradiyyar Najeriya tun lokacin dawowar mulkin a 1999.
Shugaban kasan ya yabawa jajircewar Atiku wajen hidimar al’umma da kuma ayyukan alherin sa, sannan ya roki Allah ya inganta masa lafiya.
Tinubu, ya kuma tuna lokutan da suka yi tafiyar siyasa tare wajen kafa jam’iyyar APC.














































