Home Labaru Ziyarar Aiki: Shugaba Tinubu Ya Nausa Zuwa Faransa

Ziyarar Aiki: Shugaba Tinubu Ya Nausa Zuwa Faransa

161
0
Tinubu Traveling
Tinubu Traveling

A jiya Laraba ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nausa ƙasar Faransa domin ziyarar aiki.

A wata sanarwa da mai Magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ne ya gayyaci shugaban na Najeriya.

Onanuga ya ce ziyarar ta kwana uku ce, kuma za ta mayar da hankali ne kan inganta alaƙar tattalin arziki, da dimokuraɗiyya, da noma, da tsaro, da ilimi, da kiwon lafiya, da samar da aikin yi ga matasa da dai sauran abubuwa muhimmai.

Sanarwa ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya yi tafiyar ce tare da uwargidan sa Sanata Oluremi Tinubu, inda shugaban na Faransa da uwargidan sa za su tarbe su.

Haka kuma Oluremi Tinubu da uwargidan shugaban ƙasar ta Faransa, Brigitte Macron za su gana game da shirin uwargidan shugaban Najeriya na inganta rayuwar matasa wato Renewed Hope Initiative.

Leave a Reply