Mai magana da yawun Shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya ce babu wata jihar da gwamnatin tarayya ta tilasta wa samar da Rugage domin killace dabbobin Fulani makiyaya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Garba Shehu ya ce Ruga ta na nufin wani wuri da za a tsugunar da makiyaya da masu kiwon dabbobi, kuma ba wai Fulani makiyaya ne kawai za su ci gajiyar shirin ba, duk wani mai sana’ar dabbobi zai amfana.
Rugar dai za ta kasance ta na da makarantu da asibitoci da tituna da kasuwanni da sauran abubuwan da za su taimaka wajen inganta rayuwar dabbobin makiyaya. Garba Shehu ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ba ta da niyyar kwace wa mutane filayen su ko kuma ta tursasa su yin abin da ba su yi niyya ba.