Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari zai sanar da sunayen ministocin sa a cikin watan Yuli na shekara ta 2019.
Boss Mustapha, ya ce za a kaddamar da sabuwar majalisar zartarwa ta kasa da zarar ‘yan majalisa sun koma hutu.
Ya ce shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da lamarin a gaban majalisar dokoki ta tarayya ba tare da bata lokaci ba idan sun koma hutu.Sai dai ba lallai ne a kafa majalisar zartarwar a lokacin da ake hasashe ba, musamman duba da irin barazanar da ‘yan majalisar ke yi na kaurace wa majalisar dokokin har sai an biya su hakkokin su