Home Labaru Kare Rayuka: ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Yara Tara A Zamfara

Kare Rayuka: ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Yara Tara A Zamfara

1
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta kubutar da wasu kannana yara tara da ‘yan bindiga suka sace a jihar.

A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar mai ɗauke da sa hannun kakakin ta na jihar ASP Yazid Abubakar, ya ce a ranar 3 ga watan Yuni ne rundunar ta samu bayanai daga dagacin ƙauyen Goran Namaye cewa ‘yan bindiga sun sace wasu yara maza da mata waɗanda suka tafi neman itace a jeji.

Sanarwar ta ce bayan samun labarin ne ‘yan sanda tare da hadin gwiwar jami’an tsaro suka ƙaddamar da bincike domin ceto yaran, lamarin da ya sa suka samu nasarar ceto yaran tara, tare da mayar da su hannun iyayen su.

Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo maharan tare da gurfanar da su a gaban kotu.

A ranar Asabar ne dai ‘yan bindiga suka kai hari tare da sace yaran a ƙauyen Gora da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Maradun a jihar ta Zamfara.