Home Home Kare Dalibai: Jami’ar Abuja Ta Dauki Mafarauta Aiki Don Su Yaki ’Yan...

Kare Dalibai: Jami’ar Abuja Ta Dauki Mafarauta Aiki Don Su Yaki ’Yan Bindiga

92
0
Jami’ar Abuja ta kaddamar da aikin sintiri na sa’a 24 a cikin harabar ta da kewaya ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga domin dakile ayyukan ’yan bindiga.

Jami’ar Abuja ta kaddamar da aikin sintiri na sa’a 24 a cikin harabar ta da kewaya ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga domin dakile ayyukan ’yan bindiga.

Uban Jami’ar ta Abuja, Modibbo Mohammed, ya ce an dauki matakin ne bayan harin ’yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu ma’aikata a rukunin gidajen su da ke cikin jami’ar.

Ya ce sun dauki mafarauta da ’yan banga su rika gudanar da sintiri a yankin da babu katanga saboda filin jami’ar na da girma sosai.

Uban Jami’ar ya shaida wa taron manyan shugabanni da jami’an gudanarwa da na kungiyoyin jami’ar cewa suna yin duk mai yiwuwa domin ganin ba a sake kai hari ba a jami’ar.

Da yake magana game da halin da gidajen ma’aikatan jami’ar suke ciki, ya ce, Gidajen ma’aikatan su ba su kai yadda ake bukata ba, har kunya yake ji game da irin gidajen da ma’aikatan suke zaune a ciki.

Sai dai ya ce, Kwamitin gudanarwar Jami’ar ya yi zama da Ministan Abuja a kan lamarin kuma ministan ya yi alkawarin  daukar mataki a kai, nan ba da jimawa ba.