Kotun sauraren kararrakin zaben raba gardama a majalisar jihar Kano, ta soke zaben Magaji Zarewa na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Rogo kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Dan takarar jam’iyyar PDP Jibril Falgore ne ya shigar da karar, inda ya ke kallubalanci nasarar Zarewa a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Janairu.
Sauran wadanda ya yi karar a kotun sun hada da Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta kasa INEC, da jam’iyyar APC kamar yadda wata majiya ta bayyana.
Alkalai uku a karkashin jagorancin Mai sharia A.M. Yakubu, dukkan su sun amince da soke zaben Zarewa bisa dalilin cewa, bai yi murabus daga hukumar kula da shigo da magunguna da sauran ababen sha na jihar Kano kwanaki 30 kafin zabe ba kamar yadda yake a dokar tsayawa takara ta hukumar zabe ba.
Kotun dai ta yanke hukuncin cewa, Falgore na jam’iyyar PDP ne hallastaccen zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Rogo, sannan ta umurci magatakardan majalisar jihar Kano ya rantsar da shi a matsayin zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Rogo nan take ba tare da bata lokaci ba.