Home Labarai Majalisar Wakilai Za Ta Kaddamar Da Bincike a Kan Makamai 178,000

Majalisar Wakilai Za Ta Kaddamar Da Bincike a Kan Makamai 178,000

241
0

Majalisar wakilai ta yanke shawarar kaddamar da bincike a kan lamarin makamai dubu 178 da 459 da su ka yi batan-dabo a ma’ajiyar hukumar ‘yan sandan Nijeriya a shekara ta 2019.

Wannan dai, ya biyo baya bukatar da mataimakin shugaban
masu rinjaye na majalisar Toby Okechekwu ya shigar a zauren
majalisar.

Idn dai ba a manta ba, babban mai binciken kudi na tarayya, ya
ce bincike ya nuna akalla makamai dubu 178 da 459 sun yi
batan-dabo a shekara ta 2019.

Yayin gabatar da jawabin sa, dan majalisar ya ce bincike ya
nuna adadin bindigogi samfurin AK-47 kimanin dubu 90 sun
bata ya zuwa Disamba na shekara ta 2019, ya na mai cewa daga
cikin adadin, bindigogi kirar AK-47 guda dubu 88 da 78 sun
bata a lissafi, da dogayen bindigogi da kanana dubu 3 da 907
sun bata ya zuwa watan Junairu na shekara ta 2020.

A karshe majalisar wakilai ta yi kira ga shugaban rundunar ‘yan
sandan Nijeriya ya dauki matakin gaugawa wajen kama
wadanda su ka sace makaman hukumar. yayin da ta kwamitin
harkokin ‘yan sanda aikin gudanar da bincike ya kuma kai
rahoton sa bayan makonni hudu.

Leave a Reply