Home Home Kame : Gawurtattun Masu Satar Mutane Sun Shiga Hannu A Jihar Taraba

Kame : Gawurtattun Masu Satar Mutane Sun Shiga Hannu A Jihar Taraba

63
0
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu da ta kira gawurtattun masu garkuwa da mutane 11 a Jihar Taraba da ke da ƙwace makaamai da dama.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu da ta kira gawurtattun masu garkuwa da mutane 11 a Jihar Taraba da ke da ƙwace makaamai da dama.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce mutanen suna da hannu a hare-hare da dama, ciki har da satar wani jami’in hukumar kwastam da wani ɗan uwan sarkin Jalingo da kuma ɗan sanda mai muƙamin sajen duk a Jalingo.

Kakakin ‘yan sanda Frank Mba ya ce dakarun su sun yi nasarar ƙwace bindiga tara, ciki har da AK-47 bakwai, da ɗumbin harsasai da ƙwayoyi da takunkumi yayin samamen da suka kai.

Frank Mba yace kamen waɗanda ake zargin ya biyo bayan tura rundunar gaggawa ta Intelligence Response Team zuwa Taraba domin taimaka wa ‘yan sandan Taraba wajen kawo ƙarshen satar mutane cikin gaggawa.