Home Labaru Adawa Da Juyin Mulki: Jama’a Da Dama Sun Fito Zanga-Zanga A Sudan

Adawa Da Juyin Mulki: Jama’a Da Dama Sun Fito Zanga-Zanga A Sudan

239
0
Mutane da dama ne suka fito kan tituna a Khartoum babban birnin Sudan domin nuna rashin goyon bayan su ga sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar da kuma tunawa da cika shekara uku da soma zanga-zangar da ta jawo aka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir.

Mutanen da dama sun taru a wajen kofar shiga fadar shugaban ƙasar wanda a nan ne Janar Abdel Fattah al-Burhan wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi a ƙasar a watan Oktoba yake zama.

A wurare da dama, jami’an tsaro sun harba hayaƙi mai sa hawaye da kuma gurneti mai sa kiɗimewa.

Hakazalika masu goyon bayan dimokraɗiyya na ci gaba da gudanar da tattaki a birane da dama na ƙasar.

A watan da ya gabata ne aka mayar da firaiministan ƙasar Abdallah Hamdok bayan juyin mulkin da aka yi masa a watan Oktoba.

Sai dai ƴan ƙasar Sudan da dama ba su ji daɗi ba kan cewa Mista Hamdok ya yi yarjejeniya da sojoji inda suke kira da a gudanar da mulkin dimokraɗiyya zalla.

Leave a Reply