Home Labaru Kamaru: ‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kashe Mutane 11

Kamaru: ‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kashe Mutane 11

377
0

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai wani kazamin hari cikin dare, in da suka kashe wasu mutane akalla 11 a kasar Kamaru.

Wani dan kato da gora ya tabbatar da wannan hari da aka kai a yankin Tchakamari kuma tuni maharan suka tsere bayan aika-aikar.

Bayaga kisan jama’a, ‘mayakan  sun kuma kona kauyen.

Mayakan sun shafe kimanin sa’o’i uku suna tabargaza kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar.

Tun shekara ta 2009, Kungiyar Boko Haram ke cin karanta babu babbaka a yankin tafkin Chadi da ya hada kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

Rikicin na Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 30, yayin da mutane kusan miliyan 2 suka rasa muhallansu.