Home Labaru Jan Kunne: Sarki Sunusi Ya Ce Matukar Ana Son Cigaba A Kasa...

Jan Kunne: Sarki Sunusi Ya Ce Matukar Ana Son Cigaba A Kasa Ta A Cire Son Zuciya

1161
0
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce, kiran da ake yi na a kawo gyara a Nijeriya ba zai taba aiki ba sakamakon yadda manyan ‘yan siyasa ke amfani da damar su wajen sake ruguza kasar saboda wata bukata ta su.

Sarkin Sunusi ya bayyana haka ne a lokacin wani taro da ya gudana a Abuja wanda babban malami a tsangayar nazarin addinin Islama na Jami’ar Bayero Dokta Bashir Aliyu Umar ya wakilce shi, inda ya kara da cewa ana amfani da kalmar gyara ne wajen ruguza wasu muhimman abubuwa a Nijeriya, sannan kuma ana kara ta’azzara matsalar tsaro a kasa.

Sunusi ya kuma ce, yawan son mulki da wasu  manyan ‘yan siyasa ke yi shi ne ya jefa kasar cikin rikicin kabilanci da na addini.