Home Labaru Dalilin Da Ya Sa Muka Rufe Kofar Yin Afuwa Ga ‘Yan Bindiga...

Dalilin Da Ya Sa Muka Rufe Kofar Yin Afuwa Ga ‘Yan Bindiga – Matawalle

124
0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya ce dalilin daukar matakin rufe kofar yin afuwa ga ‘yan fashin daji shi ne, ‘yan bindigar ba su yi amfani da damar da aka ba su ba a baya ba.

Matawalle ya bayyana hakan ne a karshen mako a Gusau, babban birnin jihar, inda rahotanni suka ambato shi yana cewa, a maimakon afuwa, dakarun kasar za su kawar da su ne.
Gwamnan ya ce ‘yan bindigar sun nemi a yi zaman sulhu tsakaninsu da gwamnati.
Bayanai sun yi nuni da cewa, a ‘yan kwanakin nan dakarun Najeriya sun rutsa ‘yan fashin dajin da hare-hare, lamarin da yake sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu, yayin da wasu ke tserewa zuwa jihohi da ke makwabtaka da Zamfara.
Wasu gwamnonin jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun sha gayyatar da ‘yan bindigar da su hau teburin tattaunawa, matakin da yake dorewa na dan kankanin lokaci.