Home Labaru Kaduna: Gwamnati Ta Sallami Ma’aikata 286 Daga Aiki

Kaduna: Gwamnati Ta Sallami Ma’aikata 286 Daga Aiki

44
0

Hukumar ruwa na Jihar Kaduna, KADSWAC, ta sallami a kalla mutan 286 daga cikin ma’aikatanta bayan kidaya da tattance takardun kammala makaranta da ta yi a baya-bayan nan.


Babban manajan hukumar Sanusi Maikudi, ne ya tabbatar da hakan yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kaduna.


Sanusi Maikudi, ya ce hukumar ta sallami ma’aikatan ne saboda gabatar da takardun kammala karatu na bogi bayan ta tafi makarantun da suka yi ikirarin sun kammala ta tabbatar cewa na bogi ne.


Ya ce binciken da aka yi ya nuna rashawa da ake tafkawa, cin amana, cin hanci da bannatar da kudade da ma’aikatan hukumar ke yi.


Maikudi, ya ce wannan atisayen ya zama dole duba da muhimmancin da ruwa ke da shi da kuma tsaftace muhalli.
A kan daukan ma’aikata, Maikudi ya ce bayan kammala aikin ruwan Zaria, za a dauki masu gadi 50, ma’aikata kwararru bakwai da kuma ma’aikata biyar a bangaren kasuwanci.