Home Labaru Kasuwanci Jirgin Kasan Kaduna -Abuja: Ministan Sufuri Ya Ce Zirga- Zirga Zai Dawo a Watan...

Jirgin Kasan Kaduna -Abuja: Ministan Sufuri Ya Ce Zirga- Zirga Zai Dawo a Watan Nuwamban Nan

81
0

Ministan sufuri Mu’azu Sambo ya bayyana wa manema labarai cewa zirga-zirgar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja zai dawo aiki gadan-gadan cikin wannan wata da muke ciki ta Nuwamba.

Mu’azu Sambo ya kara da cewa gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka kamata domin kada abinda ya auku a baya ya sake faruwa.

Idan ba a manta ba, ‘yan ta’adda sun kai wa jirgin kasan hari a cikin watan Maris na wannan shekara inda suka kashe wasu fasinjoji sannan suka arce da wasu da dama.

Kafin wannan lokaci, ministan sufurin, ya yi alkawarin jirgin ba zai soma aiki ba sai an saki duka wadanda ke tsare hannun ‘yan bindigan da hakan ya sa sai yanzu ne za a dawo da aikin jigilar fasinjoji a jirgin.

Tun bayan daina aiki da jirgin yayi kasuwanci da harkallar mutane masu tuka motocin haya ya tsaya cak a tasoshin shirgin.

Wasu da dama sun koka kan wahalhalu da suka afka ciki na rashin kudi saboda rashin aikin jirgin.

Wannan dawowa da Jirgin kasa yayi ya faranta wa matafiya da dama rai ganin yadda babban titin Kaduna zuwa Abuja ya yi mummunar lalacewa da bashi misaltuwa.

Leave a Reply