Home Home Jirgin Kamfanin ‘Nigeria Air’ Zai Iso Abuja Ranar Juma’a – Hadi Sirika

Jirgin Kamfanin ‘Nigeria Air’ Zai Iso Abuja Ranar Juma’a – Hadi Sirika

92
0

Ministan sufuri Sanata Hadi Sirika, ya ce jirgin sama na kamfanin ‘Nigeria Air’ zai iso Abuja ranar Juma’a mai zuwa,  wani lamari da zai zama babban ci-gaba ga shirye-shiryen soma tafiyar da harkokin kamfanin.

A wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels, ministan ya ce jirgin zai iso ne a cikin kwana biyu.

Hadi Sirika ya yi alkawarin cewa, za a kaddamar da jirgin mai kalolin tutar Nijeriya domin cika duk alkawuran da gwamnatin Buhari ta yi a bangaren sufuri.

Sai dai ya ce abin da ya rage kadai shi ne, samar da unguwanni kusa da filin jirgin wanda zuwa yanzu haka an kai kashi 60 cikin 100 na aikin.

Ya ce an kammala gina tubalin ginin, kuma su na neman gwamnati mai zuwa ta karasa aikin samar da unguwannin ta yadda zai saukaka wa mutane hawa jirgin.

Leave a Reply