Home Home DSS Ta Ce Akwai Masu Shirin Tada Zaune Tsaye A Lokacin Rantsar...

DSS Ta Ce Akwai Masu Shirin Tada Zaune Tsaye A Lokacin Rantsar Da Sabbin Gwamnatoci

282
0

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta ce akwai wasu da ke shirin tada zaune tsaye a lokacin bukukuwan mika mulki ga sabuwar gwamnati a yi a wasu jihohin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce mutanen su na son janyo wa aikin jami’an tsaro nakasu ne tare da tada hankalin jama’a su jefa tsoro ga a zukatan al’umma a lokacin bikin.

Sanarwar, wadda kakakin hukumar DSS Peter Afunanya ya fitar, hukumar ta bukaci jama’a da ‘yan jarida da kungiyoyin farar hula da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar su bi ka’idojin da aka tsara a lokacin bikin.

Haka kuma, hukumar ta shawarci jama’a su yi watsi da labarun karya ko na kanzon-kurege da na zuzuta al’umma da duk wani abu na neman razanarwa.

Hukumar DSS, ta ba jama’a tabbacin ci-gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro, domin ganin bukukuwan sun wakana lami lafiya cikin nasara a fadin Nijeriya.

Leave a Reply