Home Home Jiragen Sama 15 Sun Sauka Yayin Da Atiku Ya Kaddamar Da Kamfen...

Jiragen Sama 15 Sun Sauka Yayin Da Atiku Ya Kaddamar Da Kamfen 2023

312
0
A farkon makon nan ne, jam’iyyar PDP ta kaddamar da gangamin yakin neman zaben ta, inda akalla jiragen sama 15 su ka sauka a babban filin sauka da tashin jiragen sama na birni Uyo a jihar Akwa Ibom.

A farkon makon nan ne, jam’iyyar PDP ta kaddamar da gangamin yakin neman zaben ta, inda akalla jiragen sama 15 su ka sauka a babban filin sauka da tashin jiragen sama na birni Uyo a jihar Akwa Ibom.

Gwamnonin jam’iyyar PDP da su ka halarci taron kaddamarwar  sun hada da Daraktan yakin neman zaben Atiku Abubakar kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, da Ahmadu Umaru Fintri na jihar Adamawa da Darius Ishaku na jihar Taraba, da kuma Udom Emmanuel wanda shi ne mai masaukin baki.

Sauran sun hada da Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, da Godwin Obaseki na jihar Edo da kuma Ifeanyi Okowa.

Gwamnonin jihohin PDP da su ka kaurace wa taron kuma sun hada da Nyesom Wike, da Seyi Makinde da Samuel Ortom da Ikpeazu Okezie da kuma Ifeanyi Ugwuanyi.

Leave a Reply