Home Home Magoya Bayan Peter Obi Ba Su Isa Su Yi Tattaki A Mahaifarsa...

Magoya Bayan Peter Obi Ba Su Isa Su Yi Tattaki A Mahaifarsa Ba – Reno Omokri

341
0
Tsohon Mataimaki na Musamman ga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce magoya bayan Peter Obi na jam’iyyar LP ba su isa su yi tattaki a mahaifar dan takarar ba.

Tsohon Mataimaki na Musamman ga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce magoya bayan Peter Obi na jam’iyyar LP ba su isa su yi tattaki a mahaifar dan takarar ba.

Omokri ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce idan har maganganun da masoyan Peter ke fada cewa ya maida Jihar Anambra tamkar Aljannar Duniya babu dalilin zaman su a Jihar Legas.

Ya ce idan su na so al’umma su dauki batun sa da muhimmanci, kamata ya yi su kwashe kayan su su koma mahaifar su.

Omokri ya cigaba da cewa, tsaro da makarantu da kiwon lafiya da wutar lantarki da ake samu a Legas, yanzu haka sun fi na Jihar Anambra, kuma ma’aikatan gwamnati a Legas sun fi takwarorin su na jihar Anambra albashi mai kyau.

Leave a Reply