Home Labarai Jim’iyyar PDP Ta Karbe Ofisoshin Yakin Neman Zaben Buhari Na Katsina

Jim’iyyar PDP Ta Karbe Ofisoshin Yakin Neman Zaben Buhari Na Katsina

49
0

Jam’iyyar PDP, ta ce reshen ta na jihar Katsina ya karbe ofisoshin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari a jihar.

Shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Iyorchia Ayu ya bayyana wa manema labarai haka, ta bakin mai magana da yawun sa Yusuf Abubakar Dingyadi a Katsina, inda ya ce tuni jijiyoyin PDP sun mamaye sassa daban-daban na mahaifar shugaban kasa.

Ya ce jam’iyyar PDP ta yi matukar gazawa a jihar Katsina, lamarin da ya kara dagula rashin tsaro da talauci da rashin hadin kai da tabarbarewar tatalin arziki a jihar.

Iyorchia Ayu, ya jaddada aniyar PDP na ci-gaba da karbe bangarori da yawa a jihar Katsina, inda ya shaida wa jama’a cewa mafita gare su daga halin da su ke ciki ita ce zaben PDP a zaben shekara ta 2023.