Home Labaru Jarumta: Sojojin Nijeriya Sun Samu Nasarar Hallaka Wasu Mayakan Boko-Haram A Jihar...

Jarumta: Sojojin Nijeriya Sun Samu Nasarar Hallaka Wasu Mayakan Boko-Haram A Jihar Borno

516
0

Dakarun sojin kasa na Nijeriya karkashin  rundunar Operation halaka dodo a yankin Arewa maso gabas sun samu nasarar  kashe wasu mayakan Boko Haram a garin Gwoza da ke jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin kasa, kanal Sagir Musa ya bayyana haka, inda ya kara da cewa, lamarin ya auku ne a yayin wata arangama tsakanin sojoji da ‘yan ta’adda a lokacin da suka yi kokarin shiga dajin Sambisa.

Kanal Sagir ya ce, sojoji sun kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addana lokacin musayar wuta da aka yi tsakanin sojoji da ‘yan  ta’adda.

Wasu daga cikin kayayyakin da sojojin suka kwace daga hannub ‘yan ta’addan sun hada da makamai da wasu magunguna da za su kai wa sauran ‘yan ta’addan da suke cikin dajin.A karshe kwamandan rundunar soji ta 7 da ke jihar Borno, Birgediya Janar Abdulmalik Bulama Biu ya jinjin wa sojojin sakamakon jarumtar da su ka nuna.

Leave a Reply