Home Labaru Jam’Iyyar Labour Ta Buƙaci a Kori Shugaban INEC, Sannan A Gudanar Da...

Jam’Iyyar Labour Ta Buƙaci a Kori Shugaban INEC, Sannan A Gudanar Da Bincike

48
0

An buƙaci a gaggauta korar Shugaban Hukumar Zaɓe Mai
Zaman Kan ta ta Kasa Farfesa Mahmood Yakubu, tare da
gurfanar da shi gaban ƙuliya bisa rawar da ya taka a zaɓen
shugaban ƙasa na shekara ta 2023.

Shugaban rundunar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Akin Osuntokun ya yi wannan kira, a wajen wani taro da ya gudana a helkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Osuntokun ya kuma buƙaci a gudanar da bincike a kan duk wasu kuɗaɗe ko gudummawar da hukumar zabe ta samu kafin da lokaci da kuma bayan zaɓe.

Ya ce baya ga naira biliyan 300 da aka ware daga lalitar gwamnati, akwai kuma ƙarin wasu kuɗaɗe da kayayyakin da aka samu daga wasu hukumomi na ƙasashen waje.

Leave a Reply