Home Labaru Kasuwanci Gwamnatin Tarayya Ta Samu Tiriliyan N1.18 Daga Kudaden Haraji A Wata 6

Gwamnatin Tarayya Ta Samu Tiriliyan N1.18 Daga Kudaden Haraji A Wata 6

35
0

Gwamantin tarayya, ta samu naira tiriliyan 1 da biliyan 188 daga kudaden harajin jiki-magayi na VAT a cikin watanni shida na shekara ta 2022.

Bayanai daga hukumar kididdiga ta kasa sun nuna cewa, an samu karin sama da kashi 18 cikin 100 idan aka kwatanta da kudin haraji na tiriliyan 1 da aka samu a farkon shekara ta 2021.

Haka kuma, bayanan sun nuna cewa Nijeriya ta samu harajin VAT na naira biliyan 600 da miliyan15 a zango na biyu na shekara ta 2022, wanda ke nuni da cewa an samu karin kusan kashi 2 cikin 100 daga naira biliyan 588 da miliyan 59 da aka samu daga farkon zangon shekara ta 2022.

Hukumar NBS, ta ce harajin da aka samu na cikin gida ya kai naira biliyan 359 da miliyan 12 a zango na biyu na shekara ta 2022, sannan Nijeriya ta samu naira biliyan 111 da miliyan 13 na kudaden harajin da aka biya na waje a zango na biyu na shekara ta 2022.