Home Labarai JAM’IYYA TA BIYAR TA GARZAYA KOTU, TA CE TINUBU MAGUƊI YA YI,...

JAM’IYYA TA BIYAR TA GARZAYA KOTU, TA CE TINUBU MAGUƊI YA YI, BAI CI ZAƁEN 2023 BA

1
0

Jam’iyyar APP ta bi sahun sauran jam’iyyun da su ka garzaya
kotu, inda ta ke jayayya da nasarar da Bola Tinubu da
jam’iyyar APC su ka yi a zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta
2023.

Ɗan takarar jam’iyyar APP mai suna Osita dai ya samu ƙuri’u dubu 12 da 839, yayin da Tinubu ya samu miliyan 8 da dubiu 800, Atiku da ya zo na biyu ya damu miliyan 6 da dubu 900, sai kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour da ya samu kuri’u miliyan 6 da dubu 100.

A na shi zargin bayan ya bayyana yadda aka yi maguɗi, Osita ya buga misalai a wurare daban-daban, sannan ya kawo wasu dalilan da ya ce hujja ce mai nuna cewa Bola Tinubu bai cancanci fitowa takarar zaɓen ba ma baki ɗaya.

Daga cikin dalilan ko hujjojin sa, ya ce an yi tashe-tashen hankula a wasu yankuna, wasu wurare da dama kuma ba a yi zaɓen ba ɗungurungum.