‘Yan Majalisar Wakilan da su ka samu nasara a zaben wannan
shekarar, na ci-gaba da yunkurin neman kujerar Kakakin
Majalisar, a daidai lokacin da Jamiyyun adawa ke ganin
adadin su ya kai su tsaida wanda zai jagoranci majalisar.
Yanzu haka dai, ana cigaba da kai gwaro a kai mari, a wani yunkuri na fitar da sabbin Shugabanin Majalisar Wakilai.
Wannan dai shi ne karo na farko da za a samu Jamiyyu har takwas a majalisar, tun da aka dawo tafarkin demokradiyya a shekara ta 1999.
‘Yan jam’iyyun PDP da LP da APGAda YPP da NNPP da ADC da SDP dai, su na ganin adadin su ya kai su tsaida wanda zai jagorance su, kamar yadda mai magana da yawun jam’iyyar Labour Dakta Yunusa Tanko ya bayana.
Ya ce su ‘yan adawa da ke shirin shiga Majalisar su na da akida, kuma kokarin su shi ne su tabbatar da hadin kan ‘yan adawa domin su kafa shugabanci a majalisar, domin ta haka ne kawai su ke ganin za su kawo wa Nijeriya da al’ummar ta ci-gaba.
Daya daga cikin ‘yan Jamiyyar APC da ya ce ya fi kowa cancantar zama Kakakin Majalisar Wakilan Tajudeen Abbas, ya ce Jamiyyar APC ta na kokarin daukar mataki domin hana ‘yan adawa samun yadda su ke so.
You must log in to post a comment.