Home Home Jam’iyar PDP Zata Gyara Dukkan Abubuwan Da APC Ta Bata, Okowa

Jam’iyar PDP Zata Gyara Dukkan Abubuwan Da APC Ta Bata, Okowa

86
0
Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, kuma abokin takarar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya ce jam’iyyar su ta zaburo ne ta gyara ɓarnar da jam’iyyar APC ta yi wa ‘yan Nijeriya.

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, kuma abokin takarar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya ce jam’iyyar su ta zaburo ne ta gyara ɓarnar da jam’iyyar APC ta yi wa ‘yan Nijeriya.

Rahotanni sun ambato Okowa ya na cewa, al’ummar jihar Delta ba su bukatar mutum mai alfahari ya karbi ragamar shugabanci a zaɓen shekara ta 2023.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ƙaramar hukumar Ughelli, yayin gangamin yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan jihar Delta na jam’iyyar PDP.

A wurin gangamin yakin neman zaben ne, tsohon dan takarar da ya nemi tikitin gwamna a a karkashin jam’iyyar APC Chief Osiobe Okotie, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP tare da magoya bayan sa sama da 500.

Leave a Reply