Home Home Kotu Ta Sake Ayyana Abacha A Matsayin Dan Takarar PDP A Kano

Kotu Ta Sake Ayyana Abacha A Matsayin Dan Takarar PDP A Kano

303
0
Wata babbar kotun tarayya da ke Kano, ta yi watsi da wata kara da Jafar Bello ya shigar, inda ya ke kalubalantar zaben Mohammed Abacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP.

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano, ta yi watsi da wata kara da Jafar Bello ya shigar, inda ya ke kalubalantar zaben Mohammed Abacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP.

Jafar Bello, wanda babban abokin hamayyar Mohammed Abacha ne a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka yi a watan Mayu ya nemi a soke zaben.

Haka kuma, Jafar Bello ya yi ikirarin cewa, sunan Abacha ba ya cikin rijistar ‘yan jam’iyyar PDP a gudunmar Fagge, don haka ya ce bai cancanci tsayawa takarar zaben fidda gwanin ba.

Da ya ke zartar da hukuncin mai shari’a Abdullahi Liman, ya ce rashin sunan Mohammed Abacha a rijistar PDP bai isa ya hana shi yin takara a zaben fidda gwanin ba.

Kotun, ta yi amfani da muhawarar da lauyan Mohammed Abacha, Reuben Atabo ya yi, cewa katin shaidar kasancewa dan jam’iyyar PDP da kuma alfarmar da jam’iyyar ta yi ma shi sun isa su ba shi damar shiga zaben fidda gwani.

Leave a Reply