Home Labaru Jami’in EFCC Ya Mutu A Wurin Fada Da Abokan Aikinsa

Jami’in EFCC Ya Mutu A Wurin Fada Da Abokan Aikinsa

252
0

Wani jami’in Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa EFCC,
ya rasa ran sa a wani fada da ya barke tsakanin shi da abokan
aikin sa a Jihar Sokoto.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren, ya ce wasu jami’an hukumar uku sun kaure da fada ne bayan takaddama ta barke tsakanin su a kan ajiyar wasu kaya.

Ya ce likitocin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Danfodio da ke Sokoto ne su ka tabbatar da rasuwar jami’in mai suna Sufeto Abel Isah Dickson a ranar 7 ga watan Mayu.

Uwujaren, ya ce tuni sauran mutane biyun su na tsare a hannun ‘yan sanda bayan faruwar lamarin.

Leave a Reply