Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke birnin Kano, ta soke jarrabawar da ta shirya farawa sakamakon yajin aikin direbobin Keke NAPEP a jihar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dr. Ya’u Datti, Jami’ar ta ce an soke jarabawar da za a yi daga ƙarfe 8 zuwa 11 na safe.
Ta ce Kwamatin jarrabawar zai tattauna da shugaban jami’ar domin tsaida lokacin da za a yi sauran jarrabawar.
‘Yan ƙungiyar masu baburan da aka sani da A-Daidaita-Sahu dai sun fara yajin aikin mako ɗaya a Kano, sakamakon abin da su ka kira cin mutuncin da su ke fuskanta wajen karɓar haraji daga gwamnatin jihar.
You must log in to post a comment.