Home Home Jami’ar Abu Za Ta Fara Musayar Ilimin Aikin Gona Da Takwararta A...

Jami’ar Abu Za Ta Fara Musayar Ilimin Aikin Gona Da Takwararta A Ingila

256
0

Jami’ar Ahmadu  Bello da ke Zaria a jihar Kaduna, ta ƙulla yarjejeniya da jammi’ar Yammacin Scotland domin bunƙasa amfanin gona a nahiyar Afrika.

Daraktan yaɗa labarai na jami’ar Malam Auwal Umar, ya ce an ƙulla yarjejeniyar ne a ƙarƙashin shirin Musayar Ilimin Noma na Nahiyar Afirka.

Yace ƙawancen zai taimaka wajen musanyar ilimi a kan dabarun bunƙasa ribar ƙananan manoma da kamfanonin sarrafa amfanin gona a ƙasashen Nijeriya da Ghana da Kenya da Afirka ta Kudu.

Malam Auwal Umar, ya ce Ƙungiyar ‘yan Afirka mazauna Scotland ce ta taimaka wajen ƙulla alaƙa tsakanin jami’o’in biyu.

Leave a Reply