Home Labaru Daminar Bana: Sarkin Bauchi Ya Jagoranci Addu’ar Rokon Ruwa

Daminar Bana: Sarkin Bauchi Ya Jagoranci Addu’ar Rokon Ruwa

139
0

Mai martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu,
ya jagoranci dubban al’ummar musulmai wajen gabatar da
sallar addu’ar rokon ruwa a fadin jihar.

Manoma a jihar Bauchi dai sun koka da rashin wadataccen ruwan sama, lamarin da ke barazana ga samun damina yadda gonakai ke bukata a bana.

Masu addu’ar, sun roki taimako da gudunmawar Allah ya amince ruwan sama ya sauko wa al’ummar jihar musamman masarautar Bauchi domin samun damina mai albarka.

Da ya ke jawabi a wajen Sallar, wadda ta gudana a babban masallacin Idi da ke Bauchi, sarkin Bauchi Rilwanu Sulaiman ya bukaci al’umma su kaurace wa dukkan ayyukan sabon da ka iya janyo fushin Allah.

Ya ce dole ne a kauce wa dukkan nau’ukan sabon Allah da su ke janyo al’umma su kasa samun ni’imar sa, sannan ya bukaci jama’a su cigaba da zama cikin kwanciyar hankali domin samun ci-gaba mai ma’ana a kowane lokaci.

Leave a Reply