Home Labaru Kiwon Lafiya Jabun Magani: Hukumar NAFDAC Ta Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Taka-Tsatsan

Jabun Magani: Hukumar NAFDAC Ta Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Taka-Tsatsan

396
0

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magungunan ta kasa NAFDAC, ta bukaci mutane su yi taka-tsantsan, domin akwai jabun maganin mura da ya karade kasuwanin jihar Gombe mai suna ‘MIXAGRIP’.

Moji Adeyeye, Shugabar Hukumar
Moji Adeyeye, Shugabar Hukumar, NAFDAC

Shugabar hukumar Moji Adeyeye ta sanar da haka, inda ta ce hukumar NAFDAC ta gano jabun maganin ne a wani bincike da ta gudanar a kasuwannin jihar.

Ta ce jabun maganin baya dauke da suna da adireshin kamfanin da ya sarrafa shi a jikin kwalin maganin, domin anihin maganin ya na dauke da suna da adireshin kamfanin da ya sarrafa shi.

Moji Adeyeye, ta ce an sarrafa anihin maganin MIXAGRIP a jihar Legas ne, kuma kamfanin Orange Kalbe Limited da ke Ilupeju ne ya ke sarrafa shi. A karshe ta ce mutane da ma’aikatan kiwon lafiya, za su iya tuntubar ofishin hukumar NAFDAC mafi kusa da su domin sanar da hukumar idan aka yi kicibis da wannan magani na jabu.