Hukumar jiragen sama ta kasa NCAA, ta ce daga yau Laraba, 22, ga watan Mayu na shekara ta 2019, za ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani.
Yajin aikin dai ya fara ne da misalin karfe 5.00 na safiyar ranar Larabar nan, kamar yadda hukumar ta bada sanarwar ankarar da daukacin ‘yan Nijeriya a cikin wata sanarwa da fitar.
Wajiya majiya ta ce, hukumar ta shiga yajin aikin ne, biyo bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da ta ba gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar sufurin jiragen sama.
Rahotanni sun ce, hukumar ta yi barazanar dakile duk wata gudanarwa ta harkokin sufurin jiragen sama a fadin Nijeriya, sakamakon rashin jin dadin shimfidar wasu tsare-tsare masu dakushe kwazon ayyukan ta.A amakon da ya gabata dai, karamin ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ya bukaci hukumar ta zauna akan teburin sulhu domin warware takaddamar rashin fahimtar juna da ke tsakanin su.