Home Labaru Ishaku, Tambuwal Da Ortom Za Su Nemi Shugaban Gwamnonin PDP

Ishaku, Tambuwal Da Ortom Za Su Nemi Shugaban Gwamnonin PDP

797
0
Ishaku, Tambuwal Da Ortom Za Su Nemi Shugaban Gwamnonin PDP
Ishaku, Tambuwal Da Ortom Za Su Nemi Shugaban Gwamnonin PDP

Rahotanni na cewa, tuni an fara shirye-shiryen wanda zai zama sabon shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP.

Wata majiya ta ce, akalla gwamnoni uku ne ke burin darewa a kan kujerar da gwamna Seriake Dickson zai bari.

Masu neman kujerar kuwa sun hada da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, Darius Ishaku na jihar Taraba, da kuma Samuel Ortom na jihar Benue.

Masana kimiyyar siyasa a Nijeriya dai su na ganin cewa, kujerar ta na da matukar tasiri wajen zaben wanda jam’iyyar PDP za ta ba tikitin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Jam’iyyar PDP dai ta na da gwamnoni 15 a halin yanzu, kuma a wannan karon za ta fito da shugaban gwamnonin ta ne daga yankin Arewacin Nijeriya.

Leave a Reply