
Babban lauyan gwamnatin kasa Iran Mohammad Jafar Montazeri, ya ce hukumomin kasar su na shirin rushe rundunar ‘yan Hisbah ta kasar.
An dai samar da jami’an ne domin tabbatar da bin tsarin sanya tufafin Musulunci.
Kasar Iran dai ta na fama da mummunar tarzomr ƙin jinin gwamnati, tun bayan da wata matashiya mai shekaru 22, Mahsa Amini ta rasu a hannun ‘yan sanda.
An kama matashiyar ne, bisa zargin ta da ƙin ɗaura dan kwali ko hijabi yadda ya kamata.
Babban lauyan gwamnatin ƙasar, ya ce majalisar dokoki da kuma ɓangaren shari’a na ƙasar su na sake nazarin dokokin sanya tufafin.
You must log in to post a comment.